A na sanar da al’umma cewa yau an fara mika wuraren da za a gina sabbin makarantu kashi na farko kuma za a ci gaba har zuwa sati mai zuwa.
Akwai wasu tsare-tsare da a ka sanya da su ka shafi al’ummar da za a gina makarantun a kusa da su. Idan akwai wani matashi wanda ya kai shekara goma sha takwas (18 years) mai bukatar zama lebura wajen ginin, to shirin ya tattauna da ‘yan kwangila cewa, dole sai kashi tamanin cikin dari (80%) na ma’aikata su fito daga unuguwanni da kauyukan da ke kewaye da inda za a gina makarantun. Saboda haka a tuntubi Shugaban Al’umma Gatan Makaranta (watau SBMC Chairman) na makarantar domin bada sunayen ma su bukatar a dauke su leburori. Amma sauran ma’aikata kamar Shugaban Leburori (Mason) da sauran kwararru wajen gini to hakkin ‘dan kwangila ne ya samo su duk inda ya ke so saboda tabbatar da ingantaccen gini.
Kazalika shirin zai horas da duk leburorin domin sanin makamar aiki da sanin hakkin su wajen aikin da kuma irin dabi’un da ba za a lamunta ba. Misali, dole dan kwangila ya biya lebura hakkin sa cikin lokaci. Idan lebura ya ji ciwo wajen aiki kuma a ka tabbatar ba gangaci ba ne ko kuma shiga aikin da ba na shi ba, to hakkin ‘dan kwangila ne ya yi ma shi magani, da sauran sharudda da za a sanar da su. Lebura ya biya mai abinci kudin sa/ta ba tare da ya/ta jira an biya shi kudin aikin sa ba. Dukkan leburori za su sanya hannu a kan dokokin aiki kamin su fara. Dokokin an tanade su ne da harshen hausa domin saukin fahimta.
Idan mutanen gari na neman karin bayani to su je ofishin Ma’aikatar Ilmi na Gunduma (Zonal Office) ko na Hukumar Ilmin Bai Daya (LGEA/SUBEB) domin karin bayani. Hakkin al’umma ne su zagaya su ga yadda a ke aiyukan domin su ne wadanda za su amfana da makarantar a karon farko.
Idan akwai korafi ko tunanin an ki sanya wani wanda ya cancanta to a aiko da sako ta wannan manhajar domin isar da sakon. https://agilekatsina.org/app-release.apk
Manhajar ba ta daukar bayanin a kan mai korafin ko adireshin sa/ta ko wani bayani ba musamman.
…upon the education of the people of Katsina State the future of this State lies…